Labarai

Dram film alkalai suka shirya kawai ba zan karbi Tinubu amatsayin Shugaban Kasa ta ba ~ Aisha Yesufu

Spread the love

Fitacciyar ‘yar fafutukar kare hakkin jama’a, Aisha Yesufu, ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu, inda ta ce fim ne da alkalai suka shirya kawai.

Yesufu, wacce ta kafa kungiyar #BringBackOurGirls ta ce ba za ta taba amincewa da Tinubu a matsayin shugabanta ba saboda ya yi magudi.

Ku tuna cewa kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ya yi watsi da koken da ‘yan adawa suka saya a gabansa.

Jam’iyyun siyasa uku da suka kalubalanci nasarar shugaban su ne jam’iyyar Peoples Democratic Party, Labour Party, da Allied Peoples Movement.

Tsammani ya ce, “Na tabbatar da dawowar Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa na Tarayyar Najeriya. Jam’iyyu za su biya kudinsu.”

Da take mayar da martani game da hukuncin, Yesufu ta ce, “Tinubu bai ci zaben shugaban kasa na 2023 ba kuma ba zai taba zama shugabana ba saboda ya tafka magudi a zaben da za a ayyana shi a matsayin wanda ya samu kuri’u masu rinjaye.”

Yesufu ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo mai suna ‘Mic On’ mai taken, ‘The PEPC Judgment: Hopes met or dished’ wanda mai gabatar da shirye-shiryen Channels TV, Seun Okinbaloye, ya shirya a daren ranar Asabar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button