Kasashen Ketare

Drnal Trump Ba Dan Addinin Kirista Bane~In Ji Shugaban Kiristocin Duniya Fafaroma.

Spread the love

ayin da zaben shugaban cin kasar Amurka ke dada matsowa shugaban kasar Amurka Donal Trump na dada fuskantar kalubale daga shugabannin kasashen turawan yamma da shugabannin su ma Addinai.

Jagoran mabiya Addinin kirista na duniya fafaroma Francis ya ce Donal Trump ba Dan addinin kirista bane.

Fafaroma Francis ya bayyana haka ne yayin amsa wata tambaya da wani Dan jarida yayi masa a birnin Rome Na kasar Italia bayan dawowar Sa daga wata ziyara ta kwana 6 da yakai kasar Mexico.

Dan jaridar ya tambayi fafaroma Francis cewa ko zai shawarci mabiya cocin katolika kan Dan takarar da ya kamata su zaba.? Se fafaroma Francis yace “bazan shiga siyasa ba.”

Fafaroma Francis ya kara da cewa, shugaba Donal Trump mutum ne Wanda yayi kaurin suna a duniya wajen rudani da rikita rikita.

Fafaroma Francis yace duk wani mutum da zaiyi tunanin Gina Katanga ba gada ba tabbas wannan mutumin ba Dan addinin kirista bane.

Shugaban mabiya addinin kirista Na duniya fafaroma Francis ya kuma kawowa Dan jaridar cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya dauki alkawarin cewa zai kori baki yan gudun hijira daga kasar Amurka, tare da tilasta kasar Mexico biyan kudin Gina Katanga a iyakarta da Amurka.

Fafaroma Francis yace to duk wani mutum ko shugaba da yake kokarin Gina Katanga ba gada ba to tabbas ba Dan addinin kirista bane.

Shugaban mabiya addinin kirista Na duniya fafaroma Francis yakara nanatawa cewa tunda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya furta haka to tabbas shi ba Dan addinin kirista bane.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button