Labarai

Dubu takwas-takwas N8,000 ku’di masu yawa ga talaka ~Gwamna A.A Sule

Spread the love

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce Naira 8,000 kuɗi ne masu yawa ga iyalai da dama da ke fama da talauci wadanda ba kasafai su ke iya samun irin wannan kuɗi ba a cikin wata guda.

Gwamnan ya tunatar da cewa iyalai da yawa ne suka ci gajiyar N5,000 da Buhari ya raba a baya a matsayin tallafi, yana mai cewa matakin na yanzu ya yi daidai.

Ya ce mai yiwuwa N8,000 ba komai bane ga wasu mutane, amma kuɗi ne masu auki ga wasu da yawa daga cikin iyalai marasa galihu da ba sa ganin N8,000 duk wata.

Sule ya bayyana cewa tallafin zai yi tasiri kuma ya sauya rayuwar magidanta da dama a Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button