Labarai

Dubu talatin da shida N36,000 ake bawa Janar Janar na sojan Nageriya amatsayin Alawus na wata wata

Spread the love

Babban Hafsan Sojojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce sojojin Najeriya da Ofisoshin sojin Najeriya suna samun kasa da N50,000 a matsayin albashin wata-wata yayin da Janar-Janar da sojojin da ke aiki ke samun N1,200 domin ciyar da su a kullum.

Shugaban Rundunar wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels a yau ranar Laraba, ta ce sojojin Najeriya da hafsoshin sojan Najeriya na samun kyakykyawan tsari don haka ya kamata a rika biyansu albashin da ya dace da ayyukan da za su karfafa musu gwiwa.

A baya baya mun Sha yin rahotanni da dama kan yadda sojoji ke korafin rashin ciyarwa, rashin albashi, rashin jinya da rashin jin dadi a gaba daya duk da cewa sun yi watsi da iyalansu, lamarin da ya sanya rayuwarsu cikin kangi tare da dimbin alkawuran da gwamnatin Najeriya ta dauka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button