Labarai

Duk Da Gwamnati Ta Yafewa Tubabbun ‘Yan Boko Haram Mu Dai Ba Zamu Taba Yafe Musu Ba Har Abada, Inji ‘Yan Gudun Hijira.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

‘Yan gudun hijirar da mayakan Boko Haram suka raba da muhallansu sun bayyana cewa ba zasu taba yafewa kungiyar irin halin data sakasu a ciki ba.

Shugaban ‘yan gudun hijirar na jihar Bauchi, Buba Musa Shehu ne ya bayyana haka ga manema labarai na Guardian, hutudole ya ruwaito muku cewa Buba yace ko kadan su dai basu ga alfanun yafewa ‘yan Boko Haram ba.

Yace a yayin da su suke zaune a sansanin gudun hijira suna ta fama da kansu, wasu na mutuwa saboda yunwa da rashin kulawa amma ‘yan Boko Haram na samun kulawar da su baa basu abi bai kamata ba.

Yace a shekarar 2014 ne Boko Haram suka afkawa garinsu na Gwoza inda yace ta saman gidansa ya bi ya tsere. Munsamo muku cewa, sai yanzu ne Buba ya gano cewa ‘ya’yansa na kasar Kamaru suna gudun hijira kuma yana kokarin dawo dasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button