Labarai
Duk da harin Boko Haram Zullum ya kwana a Garin Baga ya Fara dawo da ‘yan Gudun Hijira..
Rahotannin da ke Zuwa Mana gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kwana a garin Baga duk da harin da aka kai ranar Jumma’a a kan ayarin motocinsa kuma ya karbi rukunin farkon Jama’ar Baga da Suka tsere Zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Monguno. Ya ce babu wani zagon kasa da zai hana shi aiki kuma a shirye yake ya sadaukar da kan mutanen sa.