Labarai

Duk da Obasonja ya yarda da fa’duwa a jihohin Lagos da kano amma hakan Bai Hana shi sake lashe ba a 2002 meyasa Tinubu ke son kwace kano da plateau ~Ja’afar Ja’afar.

Spread the love

Shararran Dan Jarida mawallafin Daily Nigeria Jaafar Jaafar Dake zaune a Kasar London ya bayyana takaicinsa kan yadda Shugaba Tinubu ke kokarin Saka Nageriya cikin Wani yanayi Mai muni Jaafar ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yana Mai cewa Abin mamaki ne yadda Shugaba Tinubu, wanda ke adawa da juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, ke tursasa bangaren shari’a don kawar da zababbun gwamnonin ‘yan adawa a kasarsa.

A zamanin mulkin Shugaba Obasanjo, PDP ta sha kaye a Kano da Legas a hannun jam’iyyun adawa (APP da AD), kuma hakan bai hana Obasanjo sake cin zabe ba, haka kuma PDP ta yi bayan-baya Bata shiga lamarin ba.

Kano da Plateau sune rikicin magma a Najeriya. Babu abin da ke jawo neman taimakon kai kamar zalunci. Ana zabar shugabanni ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ba wai don tada rikici ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button