Labarai

Duk direban daya sake kashe wani a Zamfara zai fuskanci Hukuncin kisa shima Matawalle

Spread the love

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi alkawarin sake farfado da matsanancin hukuncin kisa ga direbobi masu tukin Ganganci a jihar hakan biyo sakamakon hadarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane 16 a ranar Laraba da yamma. Hadarin ya faru ne a lokacin da wata babbar mota ta rasa ikonta, ta shiga cikin wasu motoci hudu wadanda ke dauke da magoya bayan Matawallen a kan hanyarsu ta Gusau / Funtua. Gwamnan ya sanar da hakan ne lokacin da ya jagoranci mambobin majalisarsa da manajan kamfanin na BUA Group a yayin ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Gusau, Alhaji. Ibrahim Bello, ranar Asabar.

Har’ila yau Gwamna Matawalle ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan bibiyu ga iyalan kowane mamacin, wanda yake da mata da kuma Naira miliyan 1 da rabi ga iyalan wadancan da ba su yi aure ba. Gwamnan ya kuma kara da cewa bawa dangin mamatan Naira dubu 50 kowanne wata daga nan harzuwa karshen mulkin sa Ya ce, gwamnatinsa za ta gabatar da tsarin rage iyaka a kan manyan hanyoyi da kuma yin gwaji a kan manyan motoci da kuma gwajin magunguna kan direbobin domin kariya daga tukin Ganganci Matawalle ya ce ya lura da cewa matakan sun zama tilas saboda haka ne zai sa direbobi ba za su sake tunanin cewa za su samu sauki ba idan suka kashe kowa, ya kara da cewa rayukan ‘yan jihar na da daraja fiye da kowane abu. Ya bukaci manajan kamfanin na BUA da su kira direbobinsu su yi masu gargadi tare da taka tsantsan a kan iyakar tuki…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button