Rahotanni
Duk gwamnan daya sake ya shigo jihata saina killace shi ~Obaseke
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya sha alwashin killace duk wani gwamnan jam’iyyar APC da yayi yunkurin shiga jihar sa don gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Yace har yanzu akwai dokar hana zirga zirga tsakanin jihohi saboda haka kowa ya zauna a mazaunin sa. Ya umurci Adams Oshiomhole, da ya cigaba da zama a Abuja idan baya so a killace shi.
Ya kuma kara da cewa dokar nan da ya haramta taruwar mutane fiye da 20 yana nan a jihar saboda haka ya zama wajibi akan jam’iyyar APC da ta kiyaye wannan dokar wurin gudanar da yakin neman zaɓe da sauran harkokinta na siyasa…