Duk Malamin Daya Bude Makarantar Islamiyya Sai Ya Fuskaci Hukunci, Inji Ganduje.
- A cewar Gwabnatin Kano
Shugaban hukumar Kula da makarantun tsangayu da makarantun islamiyoyi na jahar Kano sheikh Gwani Yahuza ‘Dan Zarga ya Gargardi malaman makarantun islamiyya da su guji bude makarantun a wannan lokaci har sai Gwabnati ta bayar da umarnin budewa.
Gwani ‘Dan zarga yayin zantawarsa da gidan rediyon freedom a birnin Kano ” yace aikin malaman islamiyya shine umarni da Aiki Mai kyau da Hana muammuna, Amma gashi suna bijirewa dokar Gwabnati suna bude makarantun” A cewar Gwani Yahuza.
Ya cigaba da cewa duk malamin islamiyyar da aka Kama ya bude makaranta to zai fuskanci fushin hukumar tasa.
A karshe ya gayyaci shugaban makarantar Salman Bin Faris dake unguwar Rijiyar Zaki zuwa hukumar Don amsa tambayoyi akan bijirewa hukumar da yayi ya bude makarantar sa.
Daga Abdulrashid Abdullahi Kano.