Siyasa

Duk Wanda Baji Tsoron Allah ba Tabbas Zaiji Tsoron wanin Allah…..

Yadda Manyan ‘Yan Siyasar Kasarnan Ke Tsoron CoronaVirus Da Haka suke Tsoron Allah Tabbas Da Kowa ya zauna Lafiya Kasa Tayi kyau.

Rashin Tsoron Allah yasa Yan Siyasa suke Cutar da Talakawa Yan siyasa Suna Ganin Komai Nasu ne Sai Yadda Sukace ayi za’ayi Duk Wanda Suke so Shi ne Zai Samu Kudi Idan Basayi da kai Zasu Tura maka EFCC, ICPC,DSS,SSS da Sauransu Dole Sai Kayi Biyayya Garesu Sannan zasu barka ka zauna Lafiya.

Kwatsam Sai Allah yayi Yadda Yayi Acikinsu Abokansu Suka Hada CoronaVirus Sai Allah ya samusu Tsoron Sa Fiyeda Komai, Kuma sai Allah ya Sa ko’ina akwai Cutar Abin sai yazama Rana Zafi Inuwa Kuna. Wannan Abu Na ciwa Yan Siyarmu Tuwo a kwarya.

Kuma basu Wa’azantu ba Suka Killace Talakawa Suka ki Tallafawa Talakawan Alhali akwai Damar Yin Hakan aka basu da Yunwa wannan kawai Ya Isa Allah ya kara Jarrabtarsu Kan Azabtarda Talakawa da Yunwa da sukeyi Yanzu Haka.

© Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button