Dukda Ni ne na lashe zabe amma zan maka jam’iyar PDP a Kotu domin ban Yarda da kuri’un da suka samu ba ~Cewar Sanata Uba sani.
Zababben gwamnan jihar Kaduna Mai jiran Rantsuwa Sanata Uba sani a wata fira da BBC Hausa a lokacin da yake amsa tambayoyi kan zaben da ya gudana a ranar Asabar wanda ya samu Nasara zama gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba sani Yasha Alwashin Kai jam’iyar PDP gaban kuliya bisa kuri’un da suka sami wanda yace kuri’un ba na zabe bane kawai kuri’u da aka rubuta.
Sanata Uba sani yace yana zaton zai Riga su Zuwa Kotu domin ba zai aminta ba Kuma da ace zabe ne akayi na Gaskiya to Tabbas da sai ya bawa jam’iyar PDP tazarar kuri’u sama da dubu sittin.
Sanata Uba sani ya sami sheda wajen taimakawa Al’ummar amatsayin sa na Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya yanzu Kuma gashi ya zama gwamnan jihar Kaduna jama’a da dama na ganin za a sami Cigaba a jihar Kaduna bisa jagorancin Sanata Uba sani amatsayin gwamnan jihar ta kaduna.