Labarai
Dukkan Mai Rai Mamaci Ne: Dan Iyan Zazzau ya rasu yana da shekaru 86.
Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan ya rasu yana da shekara 86 bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu ne da safiyar Talata a gidansa da ke Kaduna. Za a yi jana’izar sa bayan sallar Zuhr a masallacin Jumu’at na Maiduguri da ke cikin garin Kaduna.
Alhaji Yusuf Ladan, tsohon Hakimin Kabala, tsohon gogaggen mai watsa labarai ne kuma tsohon Janar Manaja na Kamfanin Watsa Labarai na Jihar Kaduna (KSMC).