Kasashen Ketare

ECOWAS Ta Bukaci Hadin Kan Sojoji Masu Juyin Mulki A Mali.

Spread the love

Shugaban kasar Niger sannan shugaban karba-karba na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka Muhammad Yusuf, ya yi kira ga sojojin da suka kwace iko a kasar Mali da su hada kai da kungiyar don ganin an dawo da mulki hannun fararen hula a cikin shekara guda.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Muhammad Yusuf yana fadar haka a jajiberen taron shuwagabannin kungiyar wanda aka gudanar a birnin Yemai babban birnin kasar.

Labarin ya kara da cewa shuwagabannin suna ganin juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Mali barazana ce ga gwamnatocinsu idan an bar abin ya ci gaba. Don haka ana saran tun bayan kammala taron, kungiyar za ta fidda rahoton bayan taron wanda zai hana da yadda suke son sojojin Mali su gaggauta maida mulki hannun farar hula da kuma baton yaduwar cutar korona a cikin kasashen na ECOWAS.

A halin yanzu dai gwamnatin rikon kwarya ta sojoji a kasar Mali ta fara tattaunawa da yan siyasa don gano yadda za ta fara shirin maida mulki a hannun fararen hula, amma ba da saurin da ECOWAS take so ba.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button