Labarai
EFCC Ta Gurfanar Da Barman A Kotu Saboda Zargin Sata.
Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ofishin reshen Ibadan, a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2020, ta gurfanar da Godwin Job (a.k.a Nifemi) a gaban Mai shari’a Bayo Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo da ke zaune a Ibadan.
An gurfanar da wanda ake kara a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na laifin sata.
Wannan tuhumar ta sabawa sashi na 399 (9) na Kundin Dokar Kare laifuka 38, Dokokin jihar Oyo.