Labarai

EFCC ta musanta kin bin umarnin Kotu akan kama Yahaya Bello

Spread the love

Dangane da cece-kuce da takaddama kan ko hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ki bin umarnin kotu game da damke tsohon gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Adoza Bello, hukumar ta musanta kin bin umarnin kotu dangane da haka.

A cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun mukaddashin daraktan hulda da jama’a na hukumar ta EFCC, Mista Wilson Uwujaren, hukumar ta nuna karara cewa duk da Bello ya nemi mafaka a matakin tabbatar da hakki ta hanyar umarnin da Mai shari’a Isa Jamil Abdullahi na babbar kotun jihar Kogi ya bayar, umarnin bai saɓa ko soke umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar na kama tsohon gwamnan da nufin gurfanar da shi a gaban kotu ba.

“Odar babbar kotun jihar Kogi ta ba da umarnin tilasta a bawa Bello ’yancin walwala, bai hana babbar kotun tarayya ta ba da wani umurni ba”, in ji shi.

Ya kuma jaddada cewa, “Hukuncin da babbar kotun tarayya ta bayar na kamo Mista Yahaya Bello domin a gurfanar da shi a gaban kotu bai ci karo da umarnin babbar kotun jihar Kogi ba. Shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya ce da ta sha bamban da matakin tabbatar da ‘yancin kai wanda ya shafi daukaka kara”.

Uwujaren ya yi nuni da cewa hukumar EFCC na da kyakkyawan tarihi wajen gurfanar da wadanda aka fallasa a siyasance kuma za ta ci gaba da gudanar da aikinta domin amfanin al’umma baki daya. Ya shawarci Bello da ya mika kansa ya amsa tuhumar da Hukumar take so a yi masa.

Ya kuma yi kira ga duk ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su bayar da goyon bayansu ga Hukumar yana mai jaddada cewa, “Hukumar EFCC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokawa da cin hanci da rashawa a doron kasa”.

Dele Oyewale
Shugaban, Media & Jama’a
Afrilu 22, 2024

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button