Labarai

EFCC Tace Faisal maina ya tsere daga hannunsu zuwa Amurka.

Faisal Maina, dan Abdulrasheed Maina, tsohon Shugaban, rusasshiyar rundinar gyara fensho, PRTT, ya gudu zuwa Amurka, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Tattalin Arziki da EFCC, ta Fadi Hakan.

Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, a ranar Alhamis, ya fada wa Mai Shari’a Okon Abang na Babban Kotun Tarayya, Abuja.

Mista Abubakar ya ce daga bayanan da ke hannun hukumar yaki da rashawa, Faisal ya shiga Amurka ta Jamhuriyar Nijar.

Tun da farko a zaman na ranar Alhamis, Mai Shari’a Abang, a cikin hukuncin ya umarci mai gabatar da belin, wanda dan majalisar wakilai ne, Sani Dan-Galadima, mai wakiltar Kaura-Namoda daga Zamfara, yayi asarar dukiyar da aka yi amfani da ita a matsayin belin Faisal din

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa an ba Mista Faisal beli na Naira miliyan 60 tare da wanda zai tsaya masa a kan wannan adadin wanda dole ne ya kasance dan majalisar wakilai mai ci.

NAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button