Labarai
EFCC tayi wani Babban kamu..
Sa’a ta kare a kan gungun wasu mutane 13 da ake zargi da aikata laifuka ta yanar gizo a ranar Alhamis 11 ga Maris, lokacin da jami’an Ofishin Shiyya na Abuja da ke EFCC suka farma maboyar su kuma suka cafke su.
An kama biyar daga cikin wadanda ake zargin a wani gida na N8m a shekara a Gilmore Estate Jahi, yayin da aka kama sauran takwas din a Katampe Extension, duk a Abuja. Wannan nasarar ta biyo bayan bayanan sirri da ake zargin su da aikatawa.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da iPhone, kwamfutar tafi-da-gidanka, kayan wasan caca, 1 Toyota Avalon da Lexus SUV. Wadanda ake zargin sun ba da bayanai masu mahimmanci kuma za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.
Daga Aliyu Adamu Tsiga