Labarai

El Rufa’i ya maka tsohon mataimakin Jonathan tare da jaridar thisday a kotu

Spread the love

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi karar Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, Mai kare hakkin bil-adama, Farfesa Chidi Odinkalu da wasu masu kare hakkin bil-adama 5. Gwamna El-Rufai na neman su biya shi tarar Naira biliyan 1.5 don zarginsu da bata masa suna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cikin kararrakin mabanbanta da lauyansa A.U. Mustapha (SAN) ya shigar a babban kotun Abuja, El-Rufai ya kuma yi karar jaridar ThisDay, Daniel Elombah, Elombah Communications, Barista Joseph Onu da Auta Nyada. A karar da ya shigar kan Omokri, El-Rufai ya ce kalaman da aka jingina masa a jaridar Thisday na ranar Lahadi 14 ga watan Yunin 2020 mai taken: ‘Sakon imel na El-Rufai na cewa ana yi wa mata masu yi wa kasa hidima da suka fito daga kudu kallon karuwai’ ya bata masa suna, ya kara da cewa ‘karya ce mara tushe da aka yi don bata masa suna.’

Gwamnan ya bukaci a biya shi Naira miliyan 500 na bata masa suna sannan a nemi afuwarsa a wallafa a jaridar. A karar da ya shigar kan Odinkalu, Daniel Elombah da Elombah Communications, El-Rufai ya ce wallafar da aka yi mai taken: ‘Jerin sunayen masu suka 25 da suka sha wahala a hannun El-Rufai da Chidi Odinkalu ya rubuta’ sannan aka wallafa a shafin Elombah.com a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 shima ‘sharri aka yi masa, ya saba doka kuma babu wani hujja.’

A wannan karar ita ma ya nemi a biya shi Naira miliyan 500 kuma a nemi afuwarsa kan ‘rubutun da ya bata masa suna sosai.’ El-Rufai ya kuma ce wata wasika da Joseph Onu da Nyada suka rubuta a ranar 19 ga watan Agustan 2020 ga shugaban kungiyoyin lauyoyi ta Najeriya (NBA) ga shugaban kungiyar Farfesa Koyinsola Ajayi, SAN, da wasu na neman janye gayyatar da aka masa na hallartar taron kungiyar shima ya ‘bata masa suna da taba mutuncinsa.’ Kazalika, El-Rufai ya bukaci a nemi afuwarsa a kuma biya shi Naira miliyan 500. Kawo yanzu Kotu ba ta tsayar da ranar fara sauraron karar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button