El Rufa’i ya sakawa masallatai da coci-coci Sharudan…
Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sabbin sharudda ga wajajen bauta wanda kuma zai fara aiki nan take, ta ce daga yanzu daga coci har masallaci kada su wuce awa daya suna bauta a cikin wajen ibadarsu.
A wata sanarwa da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya fitar da yammacin yau, Lahadi ya ce sannan wajibi ne a yi tazara a wajen sallah ko coci, sannan a sanya takunkumin fuska, a kuma rika duba zafin jikin masu shiga wajen ibadar.
Elrufai ya kuma ce daga ranar Litinin 21 ga watan Disamba 2020, duka ma’aikatan Gwamnati a jihar Kaduna daga matakin albashi na 14 zuwa kasa su zauna a gidajensu, su rika aikin daga gida.
Gwamnan dai ya ce suna daukar wadannan matakan ne domin kare yaduwar cutar korona a fadin jihar Kaduna musamman a yanzu da ake cikin zagaye na biyu na yaduwar ta. Rahotan manuniya.