Labarai

El’rufa’i Ya cika Shekaru 61 A duniya, El’rufa’i Alkharin ‘yan Nageriya ne ~Inji Uba Sani

Spread the love

El’rufa’i ya cika Shekaru 61 a Duniya Sanata Uba sani ya taya Gwamnan Jihar kaduna Malam Nasir Ahmad El’rufa’i Murnar Zagayowar Ranar haihuwarsa Sanatan ya aika da Sakon Jinjina da yabo ga Gwamnan inda ya ce Jagoranmu, maigidanmu, malaminmu kuma abokinmu ya cika shekaru 61 a yau. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya bamu irin wannan jagora mai kwarjini, amintacce kuma aboki na gaskiya.

Gwamna Nasir El-Rufai alheri ne ga jihar Kaduna da Najeriya. Ya ba da sabuwar ma’ana ga mulki da aiki a jihar Kaduna. Ya kafa Tarihi Wanda ya tsere Sa’a a jihar mu ta Hanyar Gaskiya ga aikin sadaukar da kai.

Sanatan ya Kara da Cewa A yayin da muke taya mai girma gwamna El-Rufai murnar wannan gagarumar nasarar, babban fatanmu da addu’ar mu kar ya gaza a kan kokarin da yake yi Muna fatan ya kara himma don cimma burin sa na sanya jihar Kaduna ta zama abin koyi na ci gaba.

Barka da zagayowar ranar haihuwa ga Gwamnanmu mai himma da da alkhari. Allah Ta’ala Ya ci gaba da yi muka jagoranci, da kariya da karfafawa.

Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranar haihuwa daga Sanata uba sani kaduna ta tsakiya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button