#END SARS: Wata Sabuwa Tsagerun Yankin Neja Delta Sun Goyi Bayyan Masu Zanga-Zanga
Hadin gwiwar wasu kungiyoyin ‘yan tawaye masu tayar da kayar baya a yankin Neja-Delta sun bayyana goyon bayansu ga mummunar zanga-zangar EndSARS da ke gudana a duk fadin kasar nan, suna masu cewa a shirye suke su ci gaba da yaki da kai hari kan cibiyoyin mai da iskar gas idan har gwamnatin tarayya ba ta biya bukatun matasan Nijeriya masu zanga-zangar ba.
kungiyoyin tsagerun a karkashin kungiyar ‘Reformed Niger Delta Abengers (RNDA)’ wacce ta gudanar da taron gaggawa a jihar Delta, sun kuma sanar da cewa, a shirye suke su yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin tarayya tare da shiga rundunar sojoji.
Sun kara da cewa, a cikin wata sanarwa da shugaban RNDA, mai kiran kansa Manjo-Janar Johnmark Ezonebi, wanda aka fi sani da Obama ya fitar ya ce, “Za mu shiga cikin sojojin da ke hade da shiri na ‘Operation Crocodile Smile’ kuma za mu ci gaba da kai hare-hare kan wasu cibiyoyin mai da aka gano a yankin, idan har ba a magance batun talauci, zalunci na makami da rashin daidaito a cikin yanayin rayuwa ba tsakanin ‘yan kasa da manyan ‘yan siyasa.