Labarai

EndSARS: Kungiyar Data Shirya Zanga Zangar, Ta Umarci Matasa Su Koma Gida Subi Dokar Gwamnati.

Spread the love

Dag Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Kungiyar Gamayyar Feminist Coalition, kungiyar da ke kan gaba a shirya zanga-zangar EndSARS a Najeriya, ta shawarci matasa da su hakura da zanga-zanga su zauna a gida.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafukan zumunta, kungiyar ta ce ba za ta sake karbar wata gudummawar kudi ba da sunan EndSARS sannan ta bukaci matasan da su bi dokar hana fita da gwamnati ta saka a wasu jihohin.

Ana kallon sanarwar a matsayin abin da ka iya kawo karshen jerin gwanon da matasa suka shafe mako biyu suna yi a tituna wanda kuma ya rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohi kamar Legas da Edo.

Sanarwar ta zone bayan awa biyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci matasa su dakatar da zanga-zangar, yana mai cewa cigaba da yin zanga zangar zai jawo wa tsaron kasa cikas kuma abin da ba za a amince da shi ba ne.

Kungiyar ta ce ta tara kusan dalar Amurka 400,000 na gudummawa daga sassan duniya, wadda har yanzu ba a kashe akasarinsu ba.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce jami’ansa sun gana da Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ranar Alhamis domin bayyana masa damuwarsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button