Labarai

#Endsars Lokaci yayi da Gwamnati zata dakatar da Zanga Zangar Haka~Abdulsala

Spread the love

Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar, ya bayyana zanga-zangar matasa ta #EndSARS da ke gudana a matsayin halatacciya da ta dace. Ya kuma shawarci matasa da su kasance masu kame kansu a lokacin gudanar da Zanga Zangar tasu ya Kuma  yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar da bawa matasan yancinsu ‘Yancin yin zanga-zangar AbdulsalamAbubakar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, a cikin wata sanarwa, wanda aka yi wa taken ‘zanga-zangar ENDSARS: Lokaci Ya Yi da za’a dakatar da ita Haka ya ce, “Muna kallo da matukar damuwa, bakin ciki kan abubuwan da suka faru a fadin kasar a  wadannan zanga-zangar ta matasan mu.

Mun ga munanan hotunansu  da ba su da nasaba da burin matasa masu zanga-zangar. Wannan abin bakin ciki ne matuka, amma muna kira da a kwantar da hankula a tsakanin mutanenmu tare da yin kira ga Shugaban kasa don tabbatar da cewa an mutunta ‘yan kasa da kuma kiyaye su. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button