Labarai
#Endsars Nayi matukar Bakin Ciki bisa rayukan da aka rasa biyo Bayan shigowar ‘yan Iska Cikin Zanga Zangar~Atiku
Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya rubuta a shafinsa na Twitter Yana Mai cewa Ina bakin cikin asarar rayuka biyo bayan shigowar ‘yan iska a cikin zanga-zangar lumana ta #EndSARS. Kira na ga gwamnatin da Buhari ke jagoranta shi ne kada ta fada cikin jarabar amfani da karin karfi a kan masu zanga-zangar #EndSARS Masu zanga-zangar #EndSARS ba marasa hankali ba ne; suna da manufa mai kyau kuma sun aikata abin da ya dace.
Wannan lokaci ne da za a hanzarta aiwatar da buƙatunsu da suka dace. Amfani da iyakar ƙarfi zai tsananta, maimakon hanyoyin lumana Yanzu ne lokacin da za a yi amfani da hankali, maimakon zalunci. Kuma a kan haka ne, nake kira ga Shugaban kasa da ya yi magana da Yan kasar, musamman ma matasan Nijeriya.