Rahotanni

EndSARS: Obasanjo Ya Fadawa Buhari Gaskiya A Wajan Taro Na Musamman, In Ji Fani-Kayode.

Spread the love

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya yaba wa tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo saboda ya fada wa Shugaba Muhammadu Buhari gaskiya a lokacin ganawa a ranar Juma’a.

Idan baku manta ba Buhari ya gana da tsofaffin shugabannin Najeriya da suka hada da Janar Yakubu Gowon, Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Cif Ernest Shonekan, Janar Abulsalami Abubakar, da kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Juma’a kan rikicin da ke faruwa a kasar.

Da yake bayar da cikakken bayani a cikin wani sakon Twitter a ranar Asabar, Fani-Kayode ya zargi Buhari da fadawa tsoffin shugabannin cewa #End SARS masu zanga-zangar na juya rikici a duk fadin kasar.

Ya rubuta: “Na yi farin ciki cewa OBJ ya gaya wa Buhari gaskiya a taron nasu bayan ya yi iƙirarin cewa zanga-zangar ta rikide ta zama tashin hankali.

“OBJ ya amsa ta hanyar fada masa cewa zanga-zangar ta kasance ta lumana har sai da masu daukar nauyinsu da ‘yan daba da muggan mutane suka juya kan masu zanga-zangar suka fara kai musu hari.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button