#EndSars ‘Yan Sanda Sun harbe mutun biyu su Kuma masu Zanga Zangar sun kone Ofishin Rundunar ‘yan Sandan a Legas.
Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun a ranar Talata sun kone ofishin’ yan sanda na Apapa Iganmu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 09.45 na safe, a cewar wani ganau. Shaidan gani da ido mai suna Muibudeen, ya ce ‘yan sanda sun harbi maharan kafin su cinnawa ofishin’ yan sanda wuta. Kakakin karamar hukumar Apapa-Iganmu, Ayo Micheal ya ce, Eh hakane an kai wa ofishin na ‘yan Sandan hari ofishin dake Apapa Iganmu na jihar Lagos.
Ofishin dake aiki ga dukkanin al’ummar Iganmu da ke Apapa Iganmu da kuma Orile Community a Coker /
Aguda. Micheal ya ce an kashe mutane biyu a lamarin. Ya kara da cewa, “Abin da ya faru shi ne wasu yara maza sun fito da safiyar yau. Sun hallara kansu a Orile Junction. Sun yi shirin sauka zuwa Apapa. Kamar dai jiya da suka fara a Filin jirgin saman Apapa. Suna kan hanyarsu ta zuwa Apapa, na sami labarin sun wuce ta ofishin ‘yan sanda suka yi zanga-zanga a can. “Yayin da suke zanga-zangar, jami’an‘ yan sanda sun yi yunkurin tarwatsa su. Sun yi tsayayya da ‘yan sanda. Kafin kace me, an harbi yara maza biyu a kafada da kirji. “Su biyun sun mutu, a cewar rahotanni da muka samu.”