Lafiya

#Endsars Zamu murkushe duk wani Mai kokarin kawo baraza ga hadin Kan Al’ummar Nageriya~Burtai

Spread the love

Rundunar Sojin Najeriya ta ba da gargadi a kan mutanen da ta yi wa lakabi da “masu son kawo rudani da haddasa fitina” tare da gargadin su da su guji yin hakan. Sojojin sun ce sun ci gaba da jajircewa wajen kare kasar da dimokiradiyyar ta ta kowane hali. Sanarwa Wacce za’a iya bayyana wa a matsayin gargaɗi  ga masu zanga-zangar #EndSARS, waɗanda ke mamaye tituna a  mako guda da ya gabata, suna neman a sake fasalin ‘yan sandan Najeriya,  Shugaban Sojan  Yayi barazanar “magance kowane irin yanayi cikin hanzari”. Hukumomin sojojin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Sojojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na kasar,’

Wanda mai rikon mukamin Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Col Sagir Musa ya sanya wa hannu, ran laraba. Sanarwar ta ce, “Sojojin Najeriya suna so su tabbatar wa‘ yan kasa masu bin doka da oda cewa sun himmatu ga samar da zaman lafiya, tsaro da kuma kare dimokiradiyya a Najeriya. “A matsayinta na Runduna mai daukar dawainiya da bin doka, NA ta sake tabbatar da biyayyar ta da kuma sadaukar da kai ga Shugaban kasa, kwamandan Babban Hafsan Sojojin Tarayyar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari da Tsarin Mulkin kasar. NA ta sanar da haka, ta  gargadi Kan duk masu son kawo rudani da masu tayar da hankali da su kaurace wa irin wadannan ayyukan domin har yanzu tana kan kokarin kare kasar da dimokiradiyyar ta ko ta halin kaka. “NA a shirye take ta tallafawa ƙungiyoyin farar hula gaba daya ta yadda za su kiyaye doka da oda tare da magance duk wani yanayi da ya dace.”

Hukumar sojan sun umurci hafsoshi kar su bari wasu masu adawa da dimokiradiyya da wakilan rashin hadin kai su raba hankalinsu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button