Labarai

Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Kayan Abinci Suna Saukowa Ministar Kudi Kuma Ta Ce Kayan Abinci Suna Kara Tsada.

Spread the love

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, a ranar Litinin, a wani abin da ya sabawa fadin fadar shugaban kasa, ta ce farashin kayayyakin abinci a kasarnan na hawa.

Kalaman na Ahmed sun saba da ikirarin da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu, wanda a makon da ya gabata ya ce farashin kayan abinci yana sauka.

Duk da haka, Ministar, yayin da take bayyana a shirin ‘Good Morning Nigeria’ na NTA a ranar Litinin, ya ce hakika farashin abinci yana ta tashi, ya kara da cewa, da wuya farashin abinci ya kara tashi saboda karin farashin fetur.

Ta lura, yawancin motocin dakon kayan amfanin gona suna amfani da man dizal ne ba man fetur ba.

A cewar ta, zai yi kyau idan ana iya samun tallafi kan wasu bangarori ba wai ga dukkan ‘yan Najeriya kamar yadda aka yi a gwamnatin da ta gabata ba.

Ta ce: “Gaskiya ne farashin abinci yana hauhawa kuma kamar yadda na fada a baya, tallafin mai sauki shi ne wanda ake yi kan samarwa, ba wai a kan amfani ba saboda lokacin da kake amfani da mai a motarka, ka kona shi kuma dole ka sake sakawa a motarka ka kona shi.

“Amma idan yanzu aka canza tsarin aka ce duk wata motar da zata dauki abinci ko kayan gona, farashin man dizal an bada tallafi, kayan abinci za suna zuwa kasuwa da rahusa, amma idan dai ana tallafawa tallafi ne, ko dai Man Fetur ko Wutar Lantarki, a koyaushe za a samu damar da za a samu amfani a cikin tsarin sannan kuma a koyaushe akwai gaskiyar cewa kuna tallafa wa kowa kuma ba kowa ke bukata ba. ”

Garba Shehu ya fada a makon da ya gabata cewa farashin abinci na ta faduwa, inda ya yi kira ga bakon gidan Talabijin na Channels da ya ce ba haka ba. Shehu ya ce: “Idan aka ce farashin abinci ba zai sauko ba, ina ganin malamin ya ware kansa daga kasuwa saboda mun zauna a taro aMajalisa akan Abinci, kuma mun ji jawaban masana – mutanen da suka duba kasuwannin.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button