Rahotanni

Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Rahoton Da Ke Cewa An Kai Hari A Fadar.

Spread the love

Fadar shugaban kasa ta karya wani rahoto da ake yadawa a shafukan sadarwa na zamani, dake cewa ankai Hari a fadar Shugaban Kasa dake Aso Rock Villa.

Lamarinda ya faru shine a ranar juma’a wasu jami’an tsaro dake kulawa da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari sukayi tinkari wani hadimin shugaban kasa.

Sai dai rundunar yan sanda sunyi nasarar Kama hadimin na Aisha Buhari wanda yayi harbin da sukayi a fadar ta shugaban kasa.

A nata bangaren uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bukaci da sifetan yanda da ya saki jami’in don shine ke bata kariya.

Sai dai a wata sanarwar kakakin shugaban kasa malam Garba Shehu ya fitar yace shugaba Buhari ya bayarda damar yin bincike kan wannan lamari.

Daga karshe malam Garba Shehu yaci gaba da cewa bai kamata akan wannan irin yan karamar hayani sai yan adawa su dinga ikirarin an kaiwa shugaba Buhari Hari ba, muna shaidawa yan Najeriya cewar Shugaba Buhari yana lafiya baya dauke da kowacce cuta, zancenda kuma yan adawa suke na cewa ankaimasa Hari karya ne.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button