Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Zazzafan Martani Ga Obasanjo Da Soyinka.
A Jiya laraba ne Mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mr. Pemi Adesina, yayi martani ga Kalaman Tsohon Shugaban kasa Olusegun I
Obasanjo da Marubuci Farfesa Wole Soyinka, kan kalamansu na cewa Najeriya ta samu rarrabuwar kawuna a Gwamnatin Buhari.
Adesina yace “tun kafin darewar Shugaba buhari karagar mulki Najeriya na fama da Rarrabuwar Kawuna, ba’a mulkin Buhari ne Aka samu rabuwar kawuna.`
“Tun a Shekarar 1914 da aka kirkiri Najeriya, daman kan ‘yan kasar a rabe yake domin haka Kalaman Obasanjo da Soyinka Adawace kawai ta siyasa ba komai ba.
Adesina yayi wannan jawabin ne Jiya Laraba a Gidan talbijin din (Channel TV).
Idan buku mantaba Tsohon Shugaban yace Kan ‘yan Najeriya ya rabu sosai sakamakon Gazawar Shugaba Buhari, sannan Shima Marubuci kuma Farfesa mai fashin baki Wole Soyinka ya Jaddada kalamai Irin na Tsohon Shugaban, Shine dalilin martanin na Adesina.
Ahmed T. Adam Bagas