Labarai

FANSA | Jami’an Kwastam Sun Tallawa ‘Yan Bindiga Da Buhunan Shinkafa.

Spread the love

Yadda jami’an kwastam suka baiwa ‘yan bindiga buhunan shinkafa don su kubuta daga hannun yan garkuwa.

Wani babban jami’in hukumar kwastam ta Najeriya ya bayyana yadda jami’an su suka baiwa’ yan bindiga buhu bakwai na shinkafar da suka kama don su ceci kan su daga masu aikata laifukan garkuwa da mutane.

Kwanturola Aliyu Mohammed, wanda shi ne Kodinetan sashe na 4 na rundunar hadin gwiwar sintiri a shiyyar Arewa maso Yamma, shine ya bayyana yadda lamarin ya faru yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a nihar Katsina.

Ya fadawa manema labarai cewa jami’an su dake aiki a karamar hulumar Dutsinma jihar Katsina sun bada buhunan shinkafa bakwai ga ‘yan bindiga.

Mohammed, ya bayyana cewa jami’an kwastam sun shiga daji ne inda masu shigo da shinkafa ke buya, yana mai cewa wannan ita ce hanyar da masu fasa-kwaurin ke shigowa da haramtattun kayayyaki cikin kasar.

Mu (jami’an) mun cafke buhunan shinkafa 37 kuma yan fashin sun nemi buhu bakwai kafin su basu damar wucewa su ceci rayukansu.

“Don haka, kun ga hadarin da muke dauka amma mutane, musamman wadanda ke zaune tare da al’ummomin kan iyakokin sun tsunduma cikin far wa jami’an mu,” in ji shi.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button