Farashin Man Fetur Zai Cigaba Da Karuwa Muddin Dalar Amurka Ta Tashi A Kasuwar Canji – IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta ce farashin man fetur zai ci gaba da karuwa muddin Dalar Amurka ta tashi a kasuwar canji.
Shugaban IPMAN na kasa Chinedu Okoronkwo ne ya bayyana hakan ga Jaridar DAILY POST yayin da yake mayar da martani game da rade-radin karin fam din mai.
Shugaban na IPMAN ya lura cewa farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa idan dala ta ci gaba da tashi a kasuwar saye da sayarwa.
Ya ce: “Ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci cewa idan aka cire tallafin man fetur, gwamnati ba ta kayyade farashin lita, sai dai karfin kasuwa.
Ana siya samfurin a daloli. Dala tana kusa da 890/$1 yanzu. Yayin da dala ke hauhawa, farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa.
A matsayin mafita, ya bukaci gwamnati da ta rubanya kokarin ganin an samar da iskar gas din da ‘yan Najeriya za su samu.
Ya kamata gwamnati ta yi kokarin ganin ta samar da CNG ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.
Naira ta kara faduwa zuwa dala, inda aka yi musayar ta a kan N782.38/$1 ranar Laraba a kasuwar gwamnati. Amma, a bayan fage dala a kasuwa ana siyarwa a 910/$1.
Sakamakon haka, ana sa ran farashin litar mai zai wuce N617/kowace lita.
: DailyPost