Farashin Shinkafa, Kwai Da Doya A Kudu ya Karu A Watan Aprilu — NBS

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda.

Hukumar fitarda Da Kididdiga Ta Kasa NBS, Ta Bayyana Cewar Farashin Kayayyakin Abinci a Kasarnan Musamman ma Shinkafa, Kwai, Da Doyar Kudu Sunyi Tashin Gwauron Zabi a Watan Jiya na Aprilun Da yagabata.

Hukumar Ta Bayyana Hakanne a Jawabin Da Kwararren Mai Kididdigarnan Na Tarayya, Yemi Kale, ya Fitar a shafinsa Na Twitter, a Ranar Larabar da ta Gabata.

Hukumar Ta Kara Da cewar Farashin Matsakaicin Kwai Yana Karuwa a Shekara Gudane Da Kashi 2.04 Inda a Wata guda kuma Yakan Karu Da Kashi 3.38, wato Dai Kimanin Naira 476.72, Daga Naira 461.15 dayake a Watan Maris.

Haka Zalika Farashin Matsakaicin Kwan Yana Raguwane a Shekara Da Kaso 0.98, Sannan Yana karuwa a Wata Da Kaso 4.11, Wato Naira 41. 54 a Watan Aprilu daga Naira 39.90 Dayake a Watan Maris.

Haka Zalika Rahoton ya Bayyana Cewar Farashin Kilo Guda na Shinkafa (‘Yar Buhu) a Shekara ya Karu Da Kaso 31.97 sannan a wata kuwa ya karu da kaso 7.56, wato Naira 471.84 a Watan Aprilu daga Naira 438.66 Da yake a Watan Maris,

Haka Zalika Hukumar Ta Kara Dacewar Kilo Guda Na Doyar Kudu ya Karu Da Kashi 3.48 a Shekara yayinda a wata kuwa ya karu da Kaso 11.63, Wato Naira 230.09 a Watan Aprilu Sai kuma Naira 206.12 Dayake a Watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *