Kimiya Da Fasaha

Fasahar Zamani Kashi Na Daya

Spread the love

Mu Fahimci Fasahohin Zamani (1)

A matsayinmu na wadanda suke rayuwa a wannan zamani na “information age” ya kamata mu san sababbin fasahohin da suke tashe a yanzu da kuma inda ake amfani da su da makamantansu. Akwai fasahohi da dama wadanda suka jima suna existing amma anan da dama daga cikinmu bamu sansu ba, saboda dama gwamnatin kasar tamu ba bawa computer sciences da technology muhimmanci take ba bale ma ayi tunanin kawo wani course domin amfanuwar jama’a. A yau a Nigeria bana tunanin akwai wani course na wadannan banagrori da suka wuce computer engineering, computer science, information technology da cyber security su din ma a zahirin gaskiya ba wani samun ingantaccen ilimi ake a kansu ba koda a jami’a ne.

A yau, hasashe ya nuna technology shine zai zama lamba daya na tattalin arziki a duniya duk da ma ya zama a wasu kasashen da suka cigaba. Technology ya shiga kowane field a duniya ta yadda ya zama karfen kafa a inda yake bawa taimako ta bangarori da dama. Da ace za’a dauke technology a duniya da yanzu sai dai mu koma karni na 10 ko 11 saboda tsantsar ci bayan da za’a samu a inda za’ayi asarar sama da rabi na dukiyar duniya gaba daya. Technology ya zama ruwan dare a inda ya shahara a dukkanin fanni kuma daman da yake yana tafiya da modern sciences sai ya zamanto cewa yana kutsa kowane sashe ba kakkautawa.

Dan haka akwai bukatar mu san wadanne fasahohi ne suke tashe a duniya, menene aikinsu, yaya suke, sa’annan wane irin hasashe ne akeyi a kansu. A irin wannan ankararwar ce wani yakan samu wata fasahar da tayi masa sai ya fadada bincike akai, daga karshe ma ya fada cikinta tsundum a hankali a hankali kuwa har ya zama gwani.

Barkanmu da shan ruwa sai mun hadu a kashi na biyu…

✍ Mohiddeen Ahmad
14th May, 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button