Kimiya Da Fasaha

Fasahar Zamani Kashi Na Uku.

Spread the love

Daga Mohiddeen Ahmad.

Mu Fahimci Fasahohin Zamani (3)
Cigaba…

2 Internet of Things (IoT)

Fasaha ta biyu da ya kamata mu kara sani wacce take tashe a wannan zamanin itace fasahar Internet of Things wato IoT. Ita wannan fasaha ta ta’allaka ne da fasahar yanar gizo wato so akeyi a rika daura kayayyaki (things) kamar su radio, fridge, mota, drone, electric cooker da sauransu akan yanar gizo. Abu ne wanda zai baka mamaki idan kaji ance za’a daura kayayyaki akan internet, amma ta hanyar amfani da wannan fasaha ta IoT a yau hakan mai yiwuwa ne.

Yanzu mu duba lokacin da akwai computer amma babu internet da kuma lokacin da akwai internet amma babu wayoyin nan namu na zamani. Kaga a lokacin akayi kokari aka samar da fasahar da za’a iya daura wayoyi akan internet ba wai sai computer kadai ba. Kuma mun san da cewa duk wayar da ta hau kan internet to an daura ta ne, kamar yanzu wayarka da tawa dukkaninsu an daura su akan internet yanzu (are connected to the internet). To a yanzu a wannan karni so akeyi ba wai sai wayoyi ne kawai zasu iya hawa kan internet ba, so ake ya zamanto cewa kayayyakinmu ma na (electronics) zasu iya hawa kan internet domin saukaka ayyukan yau da kullum.

Menene dalilin daura kayayyaki akan internet?
Wannan itace tambayar da mutane da dama sukeyi, kuma nasan abunda mai karatu ma ke son ji kenan. Wato a yau gaba daya burin fasahar zamani shine saukaka mana al’amuran yau da kullum ta yadda zamu rika yin abubuwanmu cikin sauki batare da mun wani wahala ba. A da zamu iya kallon labaru har a cikin gidajenmu batare da munje wani waje ba ta hanyar fasahar satellite. Da tafiya tayi tafiya sai ya zamana cewa zamu iya amfani da manyan wayoyinmu domin yin hakan da ma sauran abubuwa kamar social media, kallon labarai, kasuwanci har da karatu. Wadannan duka da ma makamantansu sun wanzu ne domin saukaka al’amuran yau da kullum.

To har ila yau fasahar IoT ta kasantu ne domin saukaka mana al’amuran mu na yau da kullum. Misali kai ne kayi packing din motarka a wani wuri kuma sai ka manta baka kulle ta ba kuma gashi har kayi nisa da ita, abunda zai fara zuwa ranka shine kada fa wani ya budeta yayi maka barna. To yanzu yaya zakayi? Shin dole sai ka koma ka rufe ta ko da kuwa kayi nisa da ita? Anan zamuce maka a’a matukar akwai fasahar IoT kuma wajen da take akwai network to kawai zaka hau wani application ne a wayarka sai ka danna mata “lock” nan take zata rufe kanta. Kada kace wannan fasahar remote control ce, a’a ai remote control yana aiki ne a inda tsakanin abubuwan babu nisa, shi kuma IoT zaiyi aiki daga nan ko zuwa ina ne kamar yadda zakayi chatting da abokinka ko da yana Switzerland ne.

Fasahar IoT a yau tayi kaurin suna a duniya duba da yadda take so ta kawo sauyi a rayuwar dan Adam. Zata taimaka mana a wajen tsaro, kasuwanci, karatu da fannoni da dama. A yau a US, China da ma sassan duniya baki daya, gidaje da kamfanoni da dama suna amfani da wannan fasaha domin saukaka abubuwan rayuwa. Misali ka dauki Jarvis wanda shugaban kamfanin Facebook ya gina, AI bot ne wanda yake hade da duk wani lungu da sako na gidanshi. Ya zame masa security ta yadda ko da ace kaje gidanshi kana kwankwasa kofa to Jarvis ne zai fara ganinka kuma bazai bude maka kofa ba har sai ya aikawa Zuckerberg tambaya cewa ga wani bako yazo gidanshi (idan kuwa ka taba zuwa ko kuwa shi(Jarvis) din ya sanka to zai fadawa Zuckerberg din cewa ga wane yazo ganinka) to sai a bashi umarnin barinsu su shigo wato ya bude musu kofa. Ba wai physical robot bane da zaka iya ganinsa, shi dai kawai yanada access da kowane lungu da sako na gidan, kama daga computer shi Zuckerberg din, da sauran abubuwan da suke dakunan gidan da sauransu.

Kwanaki Zuckerberg yace Jarvis yana fahimtar ‘yar sa (Zuck’s daughter) tana cikin damuwa har yana yi mata wasa ta hanyar bata labarun nishadi irin na yara haka. Kuma ko da ace sun fita a gida sun bar wani abu a bude kamar kofa, TV, electric cooker, AC dss to kawai sai ya hau application din ya fara chatting da Jarvis anan zai umarce shi yayi abu kaza da kaza.

Wannan itace fasahar IoT. Yanzu mun fahimci cewa fasaha ce da zata bamu damar connecting din kayayyakinmu da internet domin mu iya mu’amala dasu kai tsaye ba sai mun tashi munyi ba. Kana kwance ba sai ka tashi kaje ka danna switch ka kashe fankan dakinka ba, a’a kawai ka dauko wayarka ka danna ko ka rubuta mata “off fan” ko makamancinsa nan take zata kashe kanta. Ko kuwa idan kayi tafiya ka manta baka rufe kofar gidanka ba, da dai sauransu.

Fasahar IoT zata iya taimaka mana a fannin kiwon lafiya, tsaro, gwamnatoci, kasuwanci da sauransu. Yanzu misali zamu iya tura drone kuma mu iya controlling dinsa ko mu’amala dashi ko yana ina ne ta hanyar amfani da wannan fasaha, ko kuwa robot da sauransu.

Mu sha ruwa lafiya sai mun hadu a kashi na gaba…

Tacewa Da gabatarwa Ismail Aliyu Ubale

✍️Mohiddeen Ahmad
19th May, 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button