Labarai

Fasinjoji Sun Kone Kurmus Sakamakon Hatsarin Mota A Anambra.

Spread the love

Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa fasinjoji sun ƙone ƙurmus sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su ta yadda ba za a iya gane su ba.

Mista Andrew Kumapayi ya faɗi hakan ranar Lahadi kuma ya ƙara da cewa har zuwa yanzu ba su san takamaiman adadin waɗanda suka rasu ba saboda ƙonewar da suka yi.

Hatsarin ya faru ne ranar Lahadi a kan titin Ihiala-Onitsha a Jihar Anambra, inda abin hawansu ya kama da wuta.

A yammacin lahadi wani hatsari da ya rutsa da mota ɗaya ya faru sakamakon fashewar taya saboda tsananin gudu.

Abin hawansu ya yi alkafira sannan kuma ya kama da wuta, in ji shi.

Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa dukkanin fasinjojin sun ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba.

Daga Amir Sufi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button