Fasto ya Shigar da Karar Bankin FCMB Kotu kan Zargin Rashwa.
Limamin Cocin nan da ake zargi da hada kai da Ibrahim Magu wajen Boye kudin Sata ya Garzaya kotu, Inda Yace Bankin FCMB ta Sanya masa kudi a asusun sa da ya jayo masa Zargin Sata.
Faston me suna Emanuel Omale wanda Komitin Ayo salami ya bankado wasu kudi da aka zurara a asusunsa daga Asusun EFCC Har sama da naira Miliyan 527.
Da farko dai komitin ta gayyaci Omale tace wacce Alaka ke tsakanin sa da Magu, Yace babu wata alaka sai dai Magu yana zuwa cocin shi ya masa Addu’a, Har Ila yau an gayyaceshi karo na biyu domin sanin wacce alaka ke da akwai tsakaninsu Omale yace Babu komai sai dai lokacin da magu yake kwance a Asibitin kasar waje yaje ya masa Addu’a.
Sai dai wasu shedu sun bayyana gaban komitin cewa Sun sauya kudin cin hanci a asusun Omale bisa umarnin Ibrahim magu domin Sassauta bincike da Ake Musu a Hukumar EFCC, Wannan kudi da aka gani a asusun Omale sun zauna a Asusun har Tsawon Shekaru 4, amma Bankin FCMB tace tayi kuskuren sanya kudin a Asusun Omale ne amma ba Kudinsa bane.
Hakan ya sanya Fasto Omale ya garzaya kotu yakai karar bankin yace Bankin da tasanya kudin a asusunsa su suka jawo masa zargin boye kudin Sata.
Sai dai wasu manazarta na ganin wannan borin kunya kawai Omale yake yi, Domin Ta yaya za’a sanya Kudi har Sama da miliyan 500 tsawon Shekaru 4 bankin bata gane ba ko kuma shi Omale baije bankin ya sanar da Hakanba sai Yanzu da Shugaba Buhari ya kafa kwamitin da zai bincika Irin Ta’annati da ake zargin Ibrahim Magu ya Aikata ne, da bincike ya hau Kansu sai suka gane sunyi kuskuren Sanya kudin ne, wasu na ganin Omale ya hada kai da bankin FCMB ne domin akau da tunanin Kwamitin a kansa.
Ahmed T. Adam Bagas