Labarai

Filin masallaci Zamu Rushe duk wani Gini tunda bana uwarsa bane ~Kwankwaso

Spread the love

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya lashi takobin rushe duk wani gini da aka yi a filayen masallatan da gwamnan Kano Dr Abddullahi Ganduje ya sayarwa mutane.


A Lokacin taron rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar PDP na Kano, Sanata Kwankwaso ya nuna damuwarsa karara, kan yadda gwamnan na Kano ke yayyanka filayen masallatai yana sayarwa masu kudin jihar.


“In ba wanda Allah ya tsinewa ba wai zai rika sayar da filin masallaci?, a jihar nan har gwamnoni kiristoci mun yi, amma ba wanda ya taba mana addini sai wanda yake ikirarin shi musulmi ne” Inji Sanata Kwankwaso.


A don haka ne yace duk wanda ya sayi filin masalaci ya kwana da sanin cewa da zarar jam’iyyar PDP ta karbi mulkin Kano za su rushe duk ginin da wadanda suka saya suka yi, “Tunda ba na uwarsu bane” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button