Fina finai

Idan ku mutanen waje ba za ku auri ‘yan matanmu ba, mu za mu aure su – Mai Shadda.

Spread the love

Bashir Maishadda ya fito ne daga jihar Kano, ya shiga Kannywood kimanin shekaru 10 da suka wuce, amma a yau yana daga cikin fitattun furodusoshi a Kannywood, yana da matukar arziki kuma.

A wata hira da yayi da jaridar Blueprint ya bayyana Dalilin da yasa zai Auri ‘Yar Kannywood.

Kafin yanzu na sha wuya kafin na sami darakta nagari da yake jagorantar fina-finai na. Baabban abokina a Kannywood Ali Nuhu ne.

Na yi shirin yin aure kimanin shekara hudu da suka wuce, kuma a lokacin ina tunanin wasu jaruman Kannywood guda biyu, Aisha Aliyu Tsmaiyya da Hassana Muhammad, amma kash Tsamiyya ta yi aure sati biyu da suka wuce, kuma nan da kwanaki masu zuwa zan Auri Hassana Muhammad.

Bashir ka kara kiba kwanakin nan; menene sirrin?

Ina tunanin cewa za kuyi na yi fata sosai; saboda na shagaltu da shirye-shiryen aurena da Hassana wanda na ba ku labarin shekaru hudu da suka wuce.

Kafin mu yi maganar auren, mu tuna cewa kun yi rikici da Sarki Naziru; menene ainihin matsalar?

Aure na yana zuwa nan da ’yan kwanaki kuma a matsayinka na abokina ko dattijo ko ma uba, idan har za ka yarda da haka, ai bai kamata kayi maganar Naziru yanzu ba, saboda an daidaita lamarin. Don haka, bari muyi magana game da batutuwan da ke hannu. Na sami yarinya mai kyau kuma na shirya kashe miliyoyin Naira kamar mahaukaci don faranta mata rai. Kawo yanzu dai kun ga hotunan mu na kafin aure a shafukan sada zumunta da suka hada da akwatuna masu tsada iri-iri 13 kuma dukkansu dauke da kaya masu tsada.

To, me ya faru? Me yasa baka kara auren Tsamiyya ba?

Nayi matukar tayata farin ciki, domin bayan wadannan shekarun ta auri wanda take so. Na kasance ina yaba halayenta da kyawunta. Tana da kirki sosai, ta yi nasara a aikinta na wasan kwaikwayo kuma mace ce ‘yar kasuwa.

Jama’a suna kallon mu a Kannywood a matsayin mutanen da suka lalace. Shi yasa zan yi aure daga masana’antar. Idan ku mutanen waje ba za ku auri ‘yan matanmu ba, mu za mu aure su.

Shin nawa ka mallaka?

Na gode wa Allah da kasuwancina ke inganta a kullum. Kannywood a yanzu tana da arziki kuma muna da jarumai masu kyau da daraktoci a nan. Don Allah bayan aurena ku zo a yi min filla-filla hira. Zan ci gaba da magana har ku gaji.

Me ya sa kuka shirya shirin bikin aure a dandalin sada zumunta?

Duniya tana canzawa cikin sauri a yanzu; don haka bari mu ma mu canza da shi. Ba zan iya ɗaukar ta ko in taɓa ta a wani wuri mara kyau ba, amma na biya sadakinta. Ka ga a lokacin muna rawa tana jin kunya sosai. Don Allah a dauki abubuwa yadda suka zo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button