Kasashen Ketare
Firaministan Togo Da Mambobin Gwamnatinsa Sun Yi Murabus.
Fadar shugaban kasa a Togo ta sanar da murabus din Fira ministan kasar, Komi Sélom Klassou, da shi da illahirin mambobin gwamnatinsa.
Tuni shugaban kasar Faure Gnassingbé, ya amince da murabus din, a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar da yammacin jiya Juma’a.
Mista Gnassingbé, ya gode wa gwamnatin fira ministan mai murabus, da kuma jinjina masu kan kokarin da sukayi a bangaren tattalin arziki da siyasa da kuma na raywar al’umma duk da halin da duniya ta shiga a yanzu.
Bayanai daga kasar sun ce tun ba yau ne ba ake tsammanin nada sabuwar gwamnatin a kasar ta Togo, bayan da shugaba Gnassingbé, ya sake lashe zaben shugabancin kasar, saidai hakan bata samu saboda halin da aka shiga na annoibr korona.
Daga Comr Haidar H Hasheem Kano