Kasashen Ketare

Fraministan LebanonHassan Diab, Ya Yi Murabus.

Spread the love

Ahmed T. Adam Bagas

Wannan ya zo ne a sakamakon fashewar bam din da ya kashe kusan mutane 200 tare da wasu dubbai da suka jikkata.

Prime Firayim Minista Hassan Diab Na Lebanon da Wakiliya Anadolu ne Sukayi Murabus bayan Fashewar Wani Abu da yayi Sanadiyar Mutuwar mutane masu yawa.

Jami’an Lebanon sun ce fashewar ta faru ne yayin da wata wuta ta tashi a Inda aka adana bama-bamai, wanda aka adana a tashar jiragen ruwa ta Beirut tun shekarar 2014, duk da gargadin da wasu jami’ai suka yi cewa yana da hadari.

Da yake sanar da murabus din nasa, Diab ya ce mambobin majalisar ministocinsa sun yi murabus ne a yayin da ake ta CeCe kuce game da Irin Mummunan Kisanda Bam din yayiwa Mutane.

Ya bayyana cewa cewa cin hanci da rashawa a Lebanon ya “fi girma fiye da komai a Kasar.

“Na ayyana a yau ne zanyi murabus daga mukamina a wannan gwamnatin. Allah Ya tsare Kasar mu ta Lebanon Inji Shi.

Shugaban kasar, Michel Aoun, ya amince da murabus din Firayim Minista amma ya bukace shi da ya yi aiki da karfin gwiwa har sai an kafa sabuwar majalisar ministocin kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button