Labarai

Fusatattun Matasa Sun Lakadawa Rarara Dukan Tsiya Tare Da Kwace Motarsa A Jihar Katsina.

Spread the love

Fusatattun matasa sun lakadawa mawaki Dauda Kahutu Rarara dukan tsiya a jihar katsina, Matasan dai Yan asalin jihar katsina ne.

Aminiya ta tattara cewa wasu matasa sun kai harin ne ga mawaki a Central Market Katsina a lokacin da yake yin bidiyon sabuwar wakar sa mai suna “JAHATA CE”.

A tare dashi akwai bashir Maishadda da Tijjani Asase tare da Rarara, lokacin da Rarara ke Kan tsaka da aikin nasa sai matasan suka fusata suka fara ihu, suna la’antar mawaƙin, yayin da suke kira da harshen hausa suna “Karya ne Bamayi, Duk da cewa an hada shi da jami’an tsaro, sai dai maharan sun yi garkuwa da motar shahararren Mawakin.

A cikin wakar “JAHATA CE”, mawaƙin ya nuna rashin jin dadinsa game da tashe tashen hankalan da ake samu a jihar ta katsina duk da yawancin manyan ‘yan siyasa ciki har da shugaban ƙasa, da sauran yan siyasa da ke riƙe da manyan mukamai a ƙasar sune’ yan jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button