Labarai

Fuskokin mutun Hudu 4 Gwarzayen makaryata na 2020 A Gwamnatin Shugaba Buhari.

Spread the love

Garba Shehu shine Mai Taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari Kan harkokin yada labarai Cikin maganganun sa Kaso 80% Cikin dari 100% ‘Yan Nageriya na kallonsu a Matsayin Karya, ko a kwannan yayi magana Kan sace dalibai ‘yan Makarantar kankara mutun 344 inda Garba Shehun Yace mutun goma 10 ne Kacal aka sace Wanda daga Karshe ya Karyata kansa da kansa ya bawa Al’ummar Nageriya hakuri…

Ministar jinkai da walwalar Al’umma Hajiya Sadiya Farouq itama Jama’ar Nageriya na mata kallon Shahararriyar makaryaciya Sakamakon yawan maganganun da basu Tabbata ba, Hakan yasa ‘yan Nageriya suka saka Mata Suna zubaida, Sadiya Farouq itace ta bayyana Cewa zasu fara calliwa ‘yan Gudun Hijira abinci daga saman jirgi Haka Kuma itace ta bayyana Cewa Gwamnatin tarayya ta Raba abincin Tallafi ga ko wanne gida a Nageriya Lamarin da ‘yan Nageriya suka Karyata.

Femi Adesina Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari shima ‘yan Nageriya na Masa kallon Cikakken makaryaci Sakamakon maganganu barkatai da yake yawanyi ko a kwanakin nan Adesina Yace yanzu a Nageriya tsaro ya inganta Lamarin da ‘yan Suka Karyata…

Alh Lai Mohammed Shine Minisatan yada labarai da al’adun Nageriya shine kuma Wanda ‘yan Nageriya suka fi Kallo a Matsayin makaryaci Cikin maganganun sa Kaso %95 Cikin dari 100% ‘yan Nageriya na kallon maganarsa zancen iska zancen Karya…

Wa’yan nan mutun Hudu sune jarida mikiya ta bibiya a Matsayin mutanen da ‘yan Nageriya ke Kallo Fuskokin su a Matsayin na makaryata…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button