Labarai

Ga Fassarar Cikakkiyar Wasikar Engr. Abba K Yusuf Ga Kamfanin TEC da ya Gina Gadar kofar Nasarawa.

Spread the love

Tsohon Dan takarar Gwamna a jihar Kano Kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka Abba K Yusuf ya ce Labari ya iskemu cewar gwamnatin jihar Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai cewar an samu tasgaro da gazawar aiki wanda hakan ke barazana ga rayuwar al’umma a Gadar Sama da ke Ƙofar Nasarawa wacce aka ɓatar da miliyoyin kuɗi wajen aikinta zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Kano Sen. Rabiu Musa Kwankwaso wacce kuma aka buɗe aka fara amfani da ita a Shekara ta 2015.

Cikin zarge-zargen da gwamnati take yi hadda cewa ita wannan Gada wai tana tara ruwa wanda hakan ke janyo rubewar kankaren da akayi amfani da shi wajen aikin gadar tare da yin naso da yayyo, na san idan za ku iya tunawa Kamfanin ku ne na TEC Engineering Company Nig Ltd aka bawa aikin wannan Gadar wacce ake ta cece-kuce a kanta, sannan bisa kulawar kwararrun ma’aikata tare da Injiniyoyinku Kamfanin naku ne dai yaje har gaɓar karshe na aikin wanda kuka kammala a 2015.

Saboda haka, sabo da nauyin wannan zargi da ake yi a matsayina na tsohon Kwamishinan ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Kano wanda na kasance cikin wadanda suka fara tunanin ƙirkirar wannan gada tare da bin diddigin yadda aikinta ke gudana har izuwa lokacin da aka samu nasarar kammala ta sannan aka buɗe domin amfanin al’umma, kuma a matsayina na Ɗan kishin wannan jiha ta Kano naga ya zama wajibi kuma dole a wajena na rubuto muku wannan wasika domin na janyo hankalin ku akan ƙoƙarin ɓatawa Kamfaninku suna da ake yi tare da buƙatar Kamfanin naku da yazo yayi bincike tare da duba na tsanaki dangane da ingancin wannan gada tare da kwantar wa da mutane hankali akan ingancinta daga lokacin da aka kammala ta izuwa wannan rana da muke ciki.

Zan so ku aikomin da bayani akan binciken da na bukaci ku gabatar akan wannan gada wanda zai ƙunshi iya adadin lokacin da wannan gada za tabyi kafin ta fara samun matsala tare da dukkanin sauran bayanai a kanta wanda zai taimaka wajen kore wancan zargi na ƙarya da gwamnatin jihar Kano tayi.

Don Allah ku ɗauki wannan wasiƙa tare da dukkanin muhimmancin da ya kamata domin baiwa al’ummar gari masu bi ta kan wannan gada wacce ita ce irinta ta farko a wannan jiha kwanciyar hankali ta hanyar sanin irin inganci da kuma lokacin da wannan gada za ta yi kafin ta fara samun matsala.

Nagode
Abba Kabir Yusuf
Tsohon Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button