Ga Mutun uku 3 ‘yan Arewa mafiya farinjini
KO KUN SAN ZAFAFA UKU 3 NA AREWACIN NAGERIYA?
Yau Jaridar Mikiya tayi nazari bisa ga Bincike kuma Ta kawo maku wasu fitattun mutane uku wa’yanda suka shahara tare da farinji a shafukan sada zuminci na zamani fiye da kowa a arewacin Nageriya bisa ga mahangar Jaridar Mikiya,
Gasu Kamar Haka…
Engr Abba Kabir Yusuf wanda akafi sani da abba gida gida dan siyasa ne kuma shine yayima Jam’iyar PDP takarar gwamnan jihar Kano a 2019 Haka Zalika Shine dan Siyasa Mafi Jan hankali Tare da samun Farinji cikin karamin lokacin a wajen matasan arewa fiye da ko wanne dan siyasa…
Malam Dr Ali isah Pantami Malami ne kuma Minista za’a iya kiransa dan siyasa yanzu, iliminsa da Kwarewarsa sune sukasa yake da matukar farin jinin gun Al’ummar Nageriya idan labari nashine yana saurin daukar hankalin matasa a shafukan sada zuminci na zamani a jaridu idan su wallafa…
DCP Abba Kyari Yanzu dai shine Dan Sanda Mafi Farinji a Duk fadin tarayyar shafukan sada zuminci na Arewacin Nageriya farin jininsa bashi rasa nasaba kan jajircewarsa tare da nuna rashin tsoro gami da tunkarar ‘yan ta’adda barayin mutane dana shanu musamman anan Arewacin Nageriya…
Wannan Nazari da Binciken Jaridar Mikiya ne