Labarai

Gajiyace tayimin yawa kawai shiyasa na fa’di a lokacin da ake tantance ni a Majalisar dattijan ~Balarabe Abbas Ministan Kaduna.

Spread the love

An tantance balarabe Abbas Lawal wanda ya Fa’di a Majalisar dattijan Nageriya a lokacin tantance shi, lawal dan asalin jihar Kaduna ne tare da sauran takwarorinsa Jamila Ibrahim (Kwara) da Ayodele Olawande (Ondo), domin shiga cikin jaddawalin jerin ministoci 45 da Majalisar dattijai ta amince da su a watan Agusta.

Wannan tantancewar ya biyo bayan wasikar da shugaban kasa Bola Tinubu ya aikewa majalisar dattijai ne ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, inda ya nemi ta tabbatar da wadanda aka nada.

Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da tantancewar, al’amura sun dagule a lokacin da Lawal – na biyu da aka kira bayan Jamila Ibrahim – ya fadi bayan ya kammala gabatar da jawabinsa, lamarin da ya sa mutane da dama da ke wurin suka yi gaggawar kai masa dauki.

Bayan kusan awa daya da rufe zaman majalisar dattijai, wanda aka nada ya fito daga zauren majalisar yana murmushi Yace Ina lafiya yanzu. An yi min magani kuma ina lafiya yanzu. Asalin gajiya ce,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Yayin da dan asalin Kaduna ya kasa amsa tambayoyi saboda lamarin, an tabbatar da nadin nasa tare da sauran ‘yan uwansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button