Kungiyoyi
Gamayyar Kungiyoyin Arewa Cin Najeriya Tayi Taro A Arewa House Kaduna.
Da safiyar jiya laraba 07/10/2020 hadddaiyar kungiyar nan wacce ta tattare kungiyoyin Arewa baki daya wato CNG, ta gudanar da taro a jahar Kaduna a dakin taro na Arewa House.
Taron Wanda aka farashi tun misalin 10:00am na safiyar Wannan ranar inda aka kammala misalin karfe 3:30pm.
Taron yasamu halartar kungiyoyi da dama Wanda akalla ansamu kungiyoyi 120 daga sassa daban daban na kasar nan baki daya.
Shugaban kungiyar Alh Nastura Ashir Sharif shine ya jagoranci taron kuma ya gudanar da jawabai tare da isarwa mahalarta muhimmin saqon daya sanya aka hada taron.
Bayan kammala taron gamayyar kungiyoyin ta fitar da matsayarta akan abubuwan da suka shafi kasar nan musamman Arewa cin Najeriya baki daya.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano