Labarai

Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) Ta Shirya Yin Zanga-Zanga A Daura Mahaifar Buhari.

Spread the love

Cikin jihohi uku na gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) sun shirya shiga wani gagarumin gangami na kin jinin abinda ke faruwa a yankunan Arewa na har abada a kofar gidan Shugaba Buhari da ke Daura.

An shirya gangamin ne don yin kira ga neman a kubutar da daliban makarantar Sakandiren Kimiyya ta Gwamnati da aka sace a Kankara.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai, Kakakin Gamayyar Abdul-Azeez Suleiman ya ce sun kira shugabannin gamayyar na jahohi uku zuwa babbar hedikwatar kungiyar ta kasa an yi wa shugabannin jihohi uku da abin ya shafa bayani kan abinda akeso ayi, da kuma manufar wannan gangamin.

Ana sa ran zanga-zangar zata kunshi iyayen dukkan yaran da aka sace da sauran kungiyoyin da abin ya shafa da kuma daidaikun mutane da kuma ci gaba da zama har sai an dawo da dukkan yaran da aka sace da rai da lafiya.

Jihohin da za su fara zanga-zangar sun hada da Kano, Katsina da Jigawa. Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button