Ganduje na fuskantar kalubale daga manyan ‘yan siyasar Nageriya bayan ya furta cewa ‘yan siyasa ne Babbar matsala a tsarin zaben kasar.
Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha kakkausar suka kan cewa ‘yan siyasa ne babbar matsalar zaben Najeriya.
Wannan suka dai na fitowa ne daga manyan jam’iyyun adawa a kasar da kuma masu ruwa da tsaki a fagen siyasar kasar.
Idan dai za a iya tunawa, Ganduje a makon da ya gabata ya ce ‘yan siyasa ne babbar matsalar da ke fuskantar zabuka a Najeriya ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba kamar yadda wasu ke son yi.
Sai dai jam’iyyun adawa na ci gaba da yi wa shugaban na APC tuwo a kwarya, inda suka ce gara ya yarda cewa jam’iyyar APC da shugabanninta na kawo cikas ga nasarar zabe a Najeriya.
Daily Trust ta ruwaito cewa tun bayan komawar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, an yi ta fama da tashe-tashen hankula a zabuka, rashin tsaro, magudin zabe, sace akwatin zabe, magudi da dai sauransu.
An yi asarar rayuka da dama sakamakon rikicin zabe da ‘yan barandan siyasa ke yi. Wasu kuma an raunata su ko kuma sun ji rauni a cikin aikin. Lamarin dai ya samu karbuwa tsawon shekaru yayin da ‘yan siyasa da dama ke fafutukar neman mukaman siyasa ko tikitin jam’iyyarsu gabanin zabe. Ko a ranar zabe, ana samun kashe-kashe da dama duk da cewa an tura jami’an tsaro wuraren zabe.
Manazarta sun zayyana muhimman batutuwan da ke kara ruruta wutar rikicin da suka hada da, labarai na karya, tunzura jama’a, kalaman kyama, ayyukan raba kan malamai da rashin hakuri; kabilanci da addini; fadan cikin jam’iyya da takun saka na doka a wasu jihohi.